Uncategorized
Iwobi ya sha alwashin Najeriya za ta dau fansa a kan Guinea Bissau
Dan wasan Everton da Najeriya, Alex Iwobi ya sha alwashin cewa Najeriya za ta rama rashin nasarar da ta yi 1-0 a gida a hannun Guinea Bissau a wasan neman tikitin shiga gasar cin kofin nahiyar Afrika a ranar Juma’a.
Dan wasan Guinea Bissau, Mama Balde ne ya ci wa tawagar kasarsa kwallo daya tilo ta wasan, kwallon da ta makale har sai da aka tashi wasan.
Iwobi, wanda ke wasa a gasar Firimiyar Ingila ya ce ya zama wajibi su mayar da martini dangane da wannan ci da Guinea Bissau ta yi musu.
Ya sha alwashin cewa za su kara azama a haduwarsu ta biyu, yana mai neman goyon bayan magoya bayan tawagar ta Super Eagles don cimma haka.
Guinea-Bissau na da maki 7, Najeriya 6, Sierra Leone 2 kana Sao Tome da Principe na da maki 1 a teburin wannan fafutukar neman cancantar zuwa wasan AFCON ta 2024.
