Labarai
Wata Kotu Ta Yankewa Wasu Mutane Biyu Hukuncin Bulala 40
Wata babbar kotun shari’ar musulunchi dake gusau a jihar Zamfara ta yanke hukuncin yin bulala 40 ga Murtala Yahya Gusau da Sa’adatu Abubakar Bungudu wadanda akayi zarginsu da aikata laifin Zina a bainar jama’a a watannin 6 da suka gabata a babbar tashar Mota dake Gusau.
Alkalin kotun mai shari’a Sunusi Mohd Magami kafin yanke hukuncin yayi bita kan karar da hukumar hisbah a jihar ta shigar, inda daga karshe kotun ta ce bata samu mutanen da laifin da ake zargin su da aikatawa ba.
Sai dai mai shari’a ya ce a bisa nazarin shaidun kwamshinan shari’a na jihar ta hannun mai gabatar da kara a kotun Mustapha Muhammad Dikko, An Same Su Da Laifin Tsageranci Da Kuma Kalaman batsa, Wanda Hakan Ya Saba Da Sashi 138 Na Kundin Tsarin Shari’ar Musulunci A Jihar Zamfara.
Wannan laifi dai yana da hukunci biyu, daurin shekara daya ko kuma zabin Bulala 40 kowannen su, wanda kuma bisa zaman jiran sharia da suka yi watanni 6 ya sanya aka zartar musu da hukuncin bulalar.
Yayin ganawarsu da manema labarai matasan sun godewa Allah bisa yadda ba a same su da laifin da ake zargin su da shi ba.
Shugaban hukumar Hisbah a jihar ta Zamfara malam ashhabu Badamasi Zoma ya bayyana gamsuwa da hukuncin, ya yaba da yadda hukuncin ya kasance yana mai cewa alkalin yayi amfani da hikimah wajenyanke wannan hukunci.
Tuni dai wadanda ake zargin suka koma gidajen su bayan shafe watanni 6 na zaman jiran shari’a a gidan gyaran hali.
