Connect with us

Labarai

Jami’an DSS sun cafke ƴan fashi da masu garkuwa da mutane

Hukumar tsaro ta DSS ta ce, jami’anta sun cafke wasu ƙasurguman ƴan fashi da makami su 6 a garin Gegu Beki da ke kan hanyar Lokoja zuwa Abuja a jihar Kogi.

Hukumar ta bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa da ta fitar yau Talata.

Ta cikin sanarwar, hukumar ta ce ta samu nasarar cafke ɓata garin ne bisa haɗin gwiwar wasu takwarorinta jami’an tsaro.

Ta ce wadanda aka cafke ɗin sun haɗa da Kanal A. U. Sulaiman mai ritaya da Barista M. K. Aminu da Kabir Abdullahi da Isah Umar da kuma Kadir Echi sai Adama Abdulkarim.

Haka kuma hukumar ta DSS ta ce, ta cafke su mutanen ne tare da tarin makamai da suka haɗa da bindiga ƙirar AK47 da bindiga mai harba kanta da jigidar harsasai har ma da tsabar kuɗi Naira 11,030.

Hukumar ta ƙara da cewa, a wani aikin da ta gudanar na daban kuwa, ta samu nasarar cafke wani ƙasurgumin mai yin garkuwa da mutane Haruna Adamu, a Jihar Adamawa, da wani mai sayawa ƴan bindiga makamai Aminu Ibrahim, a kan hanyar zuwa Kubwa da ke birnin tarayya Abuja.

DSS ta ƙara da cewa, tana gab da gurfanar da waɗanda ta cafke ɗin a gaban kotu domin su gurbe abunda suka shuka.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet