Labarai
NLC da TUC sun dakatar da shirinsu na fara yajin aiki
Ƙungiyoyi ƙwadago na NLC da TUC, sun dakatar da aniyarsu ta tsunduma yajin aiki daga gobe Laraba bisa matsalar ƙarancin tsabar kuɗi da al’ummar Najeriya ke fuskanta.
Shugaban ƙungiyar NLC Joe Ajaero da kuma na TUC Festus Osifo ne suka bayyana batun janyewar yayin wani taron da suka gudanar da yammacin yau Talata a birnin tarayya Abuja.
Shugabannin sun ce, za su sanya ido tare da bibiya domin tabbatar da ganin babban bankin Najeriya CBN ya ci gaba da samar da takardun kuɗi ga bankunan kasuwanci domin sauƙaƙa wahalhalun da mutane ke fuskanta.
Haka kuma shugaban ƙungiyar NLC, ya ƙara da cewa, ƙungiyar da yake jagoranta ɗin za ta aiwatar da ƙudurinta tsunduma yajin aikin matuƙar CBN ɗin ya gaza shawo kan matsalar cikin makonni biyu masu zuwa.
