Connect with us

Labarai

EFCC Ta Gurfanar Da Tsohon Shugaban ABU Kan Zargin Badakalar Biliyan Guda

 

Tsohon Mataimakin Shugaban Jami’ar Ahmadu Bello, ABU, Farfesa Ibrahim Garba da Ibrahim Usman, an gurfanar da su a gaban kotu bisa zargin zamba.

A ranar Laraba ne mai shari’a R.M Aikawa na babbar kotun tarayya da ke jihar Kaduna ya gurfanar da tsoffin jami’an.

Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, ta gurfanar da su ne kan wasu tuhume-tuhume tara wajen karkatar da kudade sama da Naira biliyan daya.

Ana tuhumar su ne da karkatar da kudaden da aka tanada domin gyaran babban otal din Kongo Conference da ke Zariya.

Laifin, wanda aka aikata a wani lokaci a cikin watan Disambar shekarar 2013, ya saba wa Sashe na 18 (a), 15 (2) (d) na Dokar Hana badakalar Kudi ta shekarar 2011 (kamar yadda aka gyara).

Garba da Usman sun ki amsa laifin da ake tuhumar su da su.

Lauyan da ya shigar da kara, Jamil Musa, ya bukaci kotun da ta tsare su a gidan gyaran hali na Kaduna tare da sanya ranar da za a fara shari’ar.

Lauyan dake kare wadanda ake kara, M.S. Aatu, SAN, ya bukaci kotu da ta shigar da wadanda yake karewa don bayar da belinsu.

Mai shari’a Aikawa, ya bayar da belinsu a kan kudi Naira miliyan 5 tare da mutum daya wanda zai tsaya musu, amma kada yayi kasa da mataki na 15 a ma’aikatan gwamnati.

Dole ne wadanda ake tuhuma su ajiye fasfo dinsu na kasa da kasa a gaban kotu sannan su kai rahoto ga EFCC duk ranar Litinin ta farkon wata.

Mai shari’a Aikawa ya dage ci gaba da sauraron karar har zuwa ranar 20-21 ga watan Yunin 2023 domin sauraren karar.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet