Connect with us

Addini

RAMADAN: An Bukaci Musulmi Su Kara Rubanyawa Wajen Yin Sadaka – Liman

 

Wani Malamin addinin Islama da ke Abuja, Sheikh Yahya Al-Yolawi ya bukaci daukacin al’ummar Musulmi musamman masu hannu da shuni da su kara zage damtse wajen bawa mabukata agaji domin saukaka musu wahalhalun da suke fuskanta a watan Ramadan.

Al-Yolawi, wanda shi ne Babban Limamin Masallacin Nurul Yaqeen Jumma’ah Life Camp Abuja, ya bayar da wannan nasihar ne a lokacin da yake gabatar da hudubar Juma’a mai taken “Muhimmancin Ba da Sadaka a Ramadan”, ranar Juma’ar nan a Abuja.

Ya ce ba da agaji yana taimakawa wajen karfafa soyayya, fahimtar juna, taimakon juna da ‘yan uwantaka tsakanin masu hannu da shuni da talakawa a cikin al’ummar musulmi.

A cewarsa daya daga cikin kofofin da Allah ya bude wa bayinsa na samun lada mai yawa a cikin watan Ramadan ita ce ta hanyar yin sadaka.

Al-Yolawi ya ce; “Musulunci yana kwadaitar da musulmi a kodayaushe su bada sadaka da yawa musamman a cikin watan Ramadan.

“Manzon Allah s.a.w shine yafi kowa kyauta kuma ya kasance mai yawan kyauta a watan Ramadan.

“Allah Yana cewa kuma ku ciyar daga abin da Muka azurta ku da shi, kafin mutuwa ta zo wa dayanku.

“Ya ce: Ya Ubangijina! Kuma da ka jinkirta mini zuwa ga wani ajali kaɗan, sai in yi sadaka daga dukiyata, kuma in kasance daga cikin salihai.”

Ya kara da cewa za a iya yin sadaka ko kuma a yi ta ta hanyoyi daban-daban, kamar bayar da kudi ga mabukata; murmushi ko magana mai dadi ga dan uwa da ciyar da mabukata.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet