Connect with us

Featured

Sokoto: Kotu ta aike da wasu ƴan China 2 gidan yari na tsawon shekaru 3

 

Kotun daukaka kara, reshen jihar Sokoto, ta yanke wa wasu ‘yan China biyu Mista Meng Wei Kun da Mista Xu Kuai hukuncin daurin shekaru uku a gidan yari saboda samun su da laifin cin hanci da rashawa.

Jaridar Daily trust ta gano cewa tun da farko an gurfanar da wadanda ake tuhumar a gaban babbar kotun tarayya da ke zamanta a Sokoto, bisa tuhume-tuhume guda 3 da suka hadar da hada baki, halasta kudaden haram da kuma yunkurin karbar cin hanci.

An ce wadanda aka yanke wa hukuncin sun bayar da cin hancin Naira miliyan 50 ga jami’an hukumar ta EFCC shiyyar Sokoto.

Sai dai wata karamar kotu ta sallame su tare da wanke su daga tuhumar da ake yi musu wanda ya sa hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta daukaka kara.

Da yake yanke hukunci a ranar Juma’ar nan Mai shari’a Abubakar Mahmud Talba, ya ce wadanda ake kara sun yi kokarin dakile karar ta hanyar yin wasu dabaru, yana mai cewa “Lokaci ya wuce na yin amfani da wata fasaha a cikin doka”.

Ya jaddada cewa “dole ne kotun ta ba da damar a saurari karar bisa cancanta”.

A cewarsa, EFCC ta tabbatar da tuhuma ta 1 da 2 daga cikin tuhume-tuhume 3 da ake tuhuma a gaban babbar kotun tarayya ba tare da wata shakka ba amma ta amince da karamar kotun a kan kara ta 3 kuma a kan haka ta yi fatali da ita saboda irin wannan tuhumar tana gaban babbar kotun Jahar Sokoto.

“Wadanda ake kara ana tuhumar su ne da laifin hada baki da kuma biyan kudi fiye da yadda dokar hana safarar kudi ta shekarar 2011 ta tanadar kamar yadda aka yi wa Abdullahi Lawal (shugaban EFCC na shiyyar Sokoto a lokacin) wadda aka yi wa kwaskwarima a shekarar 2012 wanda aka kafa ba tare da wata shakka ba a gaban karamar kotu amma abin mamaki Alkalin kotun ya yi raddi a hukuncin da ya yanke kuma ya janye.

“Na yi nadama a ce hukuncin kamar tatsuniya ce ta alkali mai shari’a wanda ya haifar da shakku a zuciyarsa yayin da yake sauke nauyin da ke kansa.

“Ba tare da shakka ba alkali mai shari’a ya yi kuskure sosai cewa ba a aikata laifin ba,” in ji mai shari’a Talba.

Ya yi nuni da cewa, hada baki wani laifi ne na daban ko da an soke aikata laifin.

“Kuma a halin da ake ciki nan take akwai kwararan hujjojin da ba za a iya gujewa aikata laifin ba,” in ji shi.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet