Labarai
Kaduna: Sojoji sun kashe ƴan bindiga tare da ƙwato makamai a hannu su
Dakarun sojin Najeriya da suke yin aiki a runduna ta daya da ke aiki a yankin karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna, sun kashe wasu yan bindiga mutum biyar tare da kwato bindigogi kirar AK47 guda hudu tarin harsasai da adda guda daya a hannun su.
Mukaddashin mataimakin Daraktan yada labarai na rundunar Laftanar Kanar Musa Yahaya ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’ar da ta gabata.
Ya ce, dakarun sun samu nasarar ne a wannan wani bangare ne na gudanar da aikin fatattakar yan bindigar da suka addabi shiyyar Arewa maso Yammacin Najeiya.
Haka kuma ya kara da cewa an samu nasarar ne a wani samame da sojoji suka kai wuraren da suka hada da titin Kanti zuwa Tantatu da ke Dajin Kubusu da yankin Tuddan Kaso dukkansu a jihar ta Kaduna.
Sanarwar ta ce, baya ga makamai da ta samu a hannun bata garin an kuma same su da Babura guda uku da wayoyin hannu guda biyu da kuma kayayyakin aikin tsubbu.
