Labarai
Wasu Mutane Uku Za Su Fuskanci Hukuncin Rataya A Jigawa
Wata babbar kotu da ke zamanta a Kaugama a jihar Jigawa ta yanke wa Suleiman Bello, Auwalu Muhammed da Yakubu Muhammed hukuncin kisa ta hanyar rataya a kan laifuffuka tara da suka hada da hada baki, kisan kai da kuma fashi da makami ta hanyar amfani da bindigogi.
Ana zargin wadanda ake zargin sun kashe wani Audu Saje na kauyen Manda da ke karamar hukumar Kaugama a jihar tare da yin awon gaba da babur dinsa.
Haka kuma sun yi awon gaba da wata Hadiza Abdullahi da ke garin Marma a karamar hukumar Kirikasamma inda suka bukaci a biya su kudin fansa naira miliyan 150.
A wani samame da aka kai maboyar wadanda ake zargin, an samj bindigogi kirar AK-47 guda uku, GPMG daya; mujallu tara; harsashi masu rai 309; Naira 2,070,000 da babur na Marigayi Audu Saje, an ce an same su a hannun wadanda ake tuhumar.
Alkalin kotun, Mai shari’a M. M. M Kaugama, yayin da yake yanke hukuncin ya bayyana cewa, masu gabatar da kara a karkashin jagorancin babban lauyan gwamnatin jihar Jigawa, Dakta Musa Adamu Aliyu, sun yi nasarar tabbatar da laifukan da ake tuhumar wadanda ake kara na 1, 3 da 4 (Suleiman Bello). Auwalu Muhammed and Yakubu Muhammed).
Shaidu biyar sun bayar da shaida a gaban kotun.
Kotun ta ci gaba da cewa, mai gabatar da kara ya gaza tabbatar da tuhumar sata da kwace da ake yi wa wadanda ake tuhuma.
Sai dai kotun ta sallami kuma ta wanke wanda ake kara na 2 Ya’u Mai Hatsi bisa dukkan tuhume-tuhumen.
