Connect with us

Labarai

Hukumar NCC Na Wani Shiri Domin Bayar Da Taimakon A Jihohin Kasar Nan

 

Hukumar sadarwa ta kasa NCC na shirin samar da cibiyoyin sadarwa domin bayar da taimakon gaggawa a jihohi 36 na kasar nan, da kuma birnin tarayya Abuja.

Shugaban hukumar Farfesa Umar Garba Danbatta ne ya bayyana hakan a jihar Enugu ne ya bayyana hakan a jiya Asabar, yayin taron baje kolin da aka gudanar a jihar, wanda yanzu haka yake ci gaba gudana. Kamar yadda jaridar Prime Time News ta rawaito.

A cewarsa manufar samar da cibiyoyin shine cike gibin da ake samu a yankuna daban daban na kasar kan tsaikon samun taimakon gaggawa da ake da bukata daga hukumomin dake da alaqa da batun da ya taso.

Farfesa Dambatta wanda ya samu wakilcin daraktan hulda da jama’a na hukumar Mr Reuben Muoka, a yayin taron, yace ya zama wajibi kamfanonin sadarwa dake aiki a kasar nan, su samar da hanyar kira domin neman taimakon gaggawa kyauta zuwa ga muhimman bangarori ta hanyar amfani da lambobin nan guda na 112 a kowace jiha cikin jihohin kasar nan.

Sai dai ya shawarci duk masu amfani da yanar gizo da kada su bude wasikun imel da ba su saba da su ba, ya kara da cewa kada mutane su sanya bayanan sirri ta yanar gizo.

Muoka ya ce hukumar ta samar da lambar kira kyauta 622, a matsayin Mataki na biyu wanda ke baiwa masu amfani da su damar kara kaimi ga matsalolin da ba a warware su ba daga masu ba da sabis nasu ga hukumar don samun mafita mai inganci.

Shugaban ya bayyana sakonnin tes da ba a nema ba a matsayin wani babban al’amari da ke damun masu amfani da wayar, inda ya kara da cewa hukumar domin kare masu amfani da wayoyin daga wannan dabi’a ta rashin kyau ta samar da mafita mai suna.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetcasibom xcasibom xgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasibomholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet