Connect with us

Labarai

Hukumar FCTA Ta Mayar Da Mabarata A Bakin Tituna 217 Jihohin Su Na Asali

Hukumar babban birnin tarayya Abuja FCTA a ranar Lahadi ta kwaso wasu mabukata, masu yawo a tituna da ’yan maroka 217 da aka kwashe daga titin babban birnin tarayya Abuja.

Alhaji Sani Amar-Rabe, Daraktan Sashen Kula da Jin Dadin Jama’a na Sakatariyar Cigaban Jama’a (SDS) na FCTA, ya bayyana hakan a wata hira da kamfanin dillancin labarai na Kasa, NAN, a cibiyar koyar da sana’o’i da gyaran tarbiyya ta FCT da ke yankin Bwari Council.

Daraktan ya zanta da NAN jim kadan bayan tura jami’an sashen domin jigilar mabukata da mabarata zuwa jihohinsu daban-daban.

Ya yi bayanin cewa mayar da mutanen ya yi daidai da umarnin karamar ministar babban birnin tarayya Abuja, Dakta Ramatu Aliyu da babban sakatare na FCTA, Mista Olusade Adesola, wadanda suka umurci sashin kula da jin dadin jama’a da su kawar da duk wani abu da ya addabi birnin.

Ya bayyana cewar alhakin hukumar FCTA ne ta tabbatar da cewa an mayar da wadanda aka kora daga tituna zuwa jihohinsu na asali daban-daban.

“Muna nan ne dangane da mayar da marasa galihu da aka kama, masu gararamba a bakin titi, yara kanana da ’yan banga da aka ba da labarinsu, an fuskanci kalubalen kiwon lafiyarsu daidai wa daida kuma ba su nuna sha’awar koyon sana’o’i ba.

“Suna nuna sha’awar su ne kawai don halartar abin da suke ganin a matsayin ‘yanci, don ci gaba da yin abun da basu dace ba.

“Amma waɗanda suke da tunani mai kyau, suna karɓar ƙwarewa don dogaro da kai. Don haka manufar zuwanmu wannan cibiya ke nan a yau.

” A yau ba mu da yawa; Mabarata ne kawai 217 da yara kanana da za a dawo da su, galibinsu jihohin Katsina, Kaduna, Neja, Jigawa, Kano, Zamfara, Sokoto da Kebbi.

“Kuma a wannan karon muna da wasu daga jihohin Abia, Imo da Delta.”

Amar-Rabe ya bayyana cewa Karamin Ministan Babban Birnin Tarayya, Aliyu, ya tuntubi wasu daga cikin gwamnatocin Jihohin ta hanyar ofisoshinsu na hadin gwiwa, domin tabbatar da cewa jihohin da abin ya shafa sun kara kaimi wajen magance tare da kula da marasa galihu da mabaratan da aka dawo da su gida.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetgrandpashabetmarsbahismarsbahismarsbahisholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahisjojobetholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet