Connect with us

Labarai

Niger: Jami’an Yan Sanda Sun Kama Mutane Biyu Da Suka Hallaka Wani Dan Sanda

 

Wasu mutane biyu da ake zargin sun hallaka wani jami’in dan sanda mai suna Nasiru Yusuf, yanzu haka sun fada komar ‘yan sanda a jihar Neja.

Wadanda ake zargin sun aikata laifin ne a kauyen Minima da ke karamar hukumar Lavun a jihar.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar DSP Wasiu Abiodun ne, ya bayyana hakan a ranar Lahadin data gabata cewa lamarin ya faru ne lokacin da maharan suka far wa wasu jami’an ‘yan sanda guda biyu da ke bakin aiki a yankin.

A cewarsa, “Akwai korafin cin zarafi a yankin kuma an yi wa ‘yan sanda biyu cikakken bayani a wurin da lamarin ya faru a kauyen Minima domin gudanar da bincike tare da kama su.”

Ya kara da cewa, ana cikin haka ne mutanen kauyen suka far wa ‘yan sandan biyu, inda suka yi musu raunuka, sannan ya jaddada cewa an kai su cibiyar kula da lafiya ta tarayya da ke Bida domin yi musu magani, wanda daga bisani an tabbatar da mutuwar daya daga cikinsu PC Nasiru Yusuf a asibitin, yayin da dayan ke ci gaba da karbar magani.

Kakakin ya kuma bayyana cewa, mutanen biyu da aka kama da hannu a cikin lamarin, a halin yanzu ana ci gaba da yi musu tambayoyi, inda ya jaddada cewa ana gudanar da bincike kan lamarin.

Abiodun ya bayyana cewa bayan kammala bincike, mutanen biyu za su bayyana a gaban kotu.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetgrandpashabetmarsbahismarsbahismarsbahistipobettipobetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahisjojobettipobetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet