Connect with us

Labarai

Kano: NDLEA Ta Cafke Wasu Mutane 352 Kan Zargin Ta’ammali Da Muggan Kwayoyi

 

Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA ta cafke wasu mutane 352 tare da kama tan 2.1 na haramtattun kwayoyi a jihar Kano.

Kwamandan NDLEA a jihar, Mista Abubakar Idris-Ahmad ne ya bayyana hakan a wata hira da kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN a Kano ranar Alhamis.

Idris-Ahmad ya ce an kama mutanen ne a tsakanin watan Janairu zuwa Maris.

Ya ce wadanda ake zargin sun hada da maza 208 da mata 44, yayin da magungunan da aka kama sun hada da kilogiram 955.304 na tabar wiwi, da Codeine da Tramadol kilogiram 1,225.05.

Sauran a cewarsa sun hada da gram 25 na hodar iblis, giram 17 na ganye mai sa maye da kuma giram 52 na methamphetamine.

Kwamandan ya ce babban kalubalen da ke gaban hukumar a jihar shi ne shawo kan al’umma wajen bankado masu safarar miyagun kwayoyi a tsakaninsu.

Kalubalen mu shine samun damar ilimantar da al’ummomi don samar da bayanai masu amfani game da maboyar masu shan muggan kwayoyi ko dillalan da ayyukansu suka ci gaba da yin illa ga al’umma.

“Ya kamata mutane su san illolin da masu amfani da muggan kwayoyi ko masu safarar miyagun kwayoyi ke haifarwa a cikin al’umma ta yadda jama’a za su fito da bayanai masu amfani don tabbatar da al’ummar da ba ta da miyagun kwayoyi,” inji Idris-Ahmad.

Don haka ya yi kira ga jama’a da su rika bayar da bayanai masu amfani kuma a kan lokaci kan masu safarar miyagun kwayoyi ga rundunar, ta yadda za a fitar da su daga yawo da kuma kare al’umma.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet