Labarai
Ƴan bindiga sun sace Tsohon Gwamnan Nasarawa
Rundunar ƴan sandan jihar Nasarawa, ta tabbatar da rahoton sace Tsohon matainmakin Gwamnan jihar farfesa Onje Gye-Wado.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar DSP Ramhan Nansel, ne ya tabbatar wa da manema labarai faruwar lamarin yana mai cewa, an yi garkuwa da shi ne da safiyar yau Juma’a.
Ya ce an yi awon gaba da tsohon mataimakin gwamnan ne lokacin da ƴan bindigar suka kutsa cikin gidansa da ke ƙauyen Gwagi a karamar hukumar Wamba na jihar.
Mai magana da yawun ƴan sandan ya ce haɗin gwiwar ƴan sanda da wasu jami’an tsaro suna can suna ci gaba da bin sawun maharan da nufin ceto wanda aka yi garkuwa da shi.
