Connect with us

Labarai

Hukumar NPC Za Ta Horas Da Ma’aikata 5,000 Don Gudanar Da Aikin Kidayar 2023

 

Hukumar kula da kidayar jama’a ta kasa NPC, za ta horas da ma’aikata 5,000 domin gudanar da kidayar jama’a da gidaje ta shekarar 2023 a jihar Adamawa.

Ma’aikatan sun hada da ma’aikata na dindindin da kuma ma’aikatan wucin gadi don yin atisayen a kananan hukumomi 21 na jihar.

A ranar Alhamis mai zuwa ne 13 ga watan Afrilu za a fara horo a matakin kananan hukumomi a dukkan kananan hukumomi 21 dake jihar.

Kwamishinan NPC na jihar Adamawa, Dakta Clifford Zirra, ya tabbatar da cewa ma’aikatan na dindindin da na wucin gadi 5,000 za su samu horon nan da kwanaki bakwai.

Ya kara da cewa hakan na zuwa ne bayan kwashe kwanaki bakwai na gudanar da aikin tantance ingancin bayanai da horar da ma’aikata na musamman da hukumar ta shirya a duk jihohin tarayya da babban birnin tarayya Abuja FCT.

Jami’in NPC ya kuma bayyana cewa shirin horas da ma’aikatan da aka shirya zai gudana a lokaci guda a fadin jihohi 36 na tarayya da kuma babban birnin tarayya Abuja.

DAILY POST ta ba da rahoton cewa ƙidayar 2023, wanda aka shirya kidaya kowane mutum, gida da tsare-tsare na kasa da aiwatar da ayyuka, za a fara yin sa a wata mai zuwa.

An shirya atisayen na kwanaki uku a ranakun 3, 4 da 5 ga watan Mayu.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetDeneme Bonusu Veren SitelerCasibomcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetgrandpashabetmarsbahismarsbahismarsbahisjojobetjojobetjojobetjojobet girişmarsbahisjojobetgrandpashabetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabet girişjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahisjojobetjojobetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet