Connect with us

Labarai

Tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Nasarawa Da Aka Sace Ya Samu ‘Yanci

An sako Farfesa Onje Gye-Wado, tsohon mataimakin jihar Nasarawa, wanda aka yi garkuwa da shi a daren ranar Alhamis bayan an biya kudin fansa naira miliyan hudu ya samu ‘yanci.

Idan dai za a iya tunawa, an yi garkuwa da farfesan shari’a ne daga gidan sa da ke Rinza, kusa da Wamba, shedikwatar karamar hukumar Wamba ta jihar.

Masu garkuwa da mutanen sun bukaci a biya su kudin fansa Naira miliyan 70, amma iyalan sun tattauna daga Naira miliyan 2, daga baya kuma suka biya Naira miliyan 3.5, inda a karshe suka biya Naira miliyan 4 kafin a sako shi.

Wata majiya ta dangin ta ce, “Masu garkuwa da mutanen sun karbi kudin fansa ne a kusa da makarantar Sakandiren Mada Hills da ke Akwanga, tare da cajin katin naira 200, bayan sun sako shi daga sansaninsu da ke kusa da Angwan chiyawa, kusa da tsaunukan da ke tsakanin Akwanga da Nasarawa Eggon.”

An tattaro cewa an mayar da Farfesa Gye-Wado fadar sarkin Wamba, a Oriye Rindre, da ke Justice Lawal Musa Nagogo, bayan an sake shi.

Jaridar Solacebace ta rawaito cewa Wani tsohon shugaban kungiyar yan jaridu NUJ kuma tsohon kwamishinan yada labarai a jihar, Mista Dogo Shamma, ya tabbatar da sakin Farfesa Gye-Wado, ta hanyar sakon waya.

“In sha Allahu Mai Girma Farfesa Onje, a karshe an sako shi daga hannun masu garkuwa da mutane a yanzu, wato ranar Lahadi da daddare.”

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet