Labarai
Zamfara: Ƴan sanda sun ceto mutane 9 daga hannun ƴan bindiga
Rundunar ƴan sandan jihar Zamfara, ta ce, ta ceto wasu mutane tara da masu garkuwa da mutane suka sace.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar CSP Muhammad Shehu, ne ya bayyana hakan a Gusau babban birnin jihar.
Ya ce, an ce mutanen ne ranar 11 ga wannan watan da muke ciki na Afrilu a yankin ƙaramar hukumar Tsafe.
Haka kuma ya ƙara da cewa, mutanen da aka ceto ɗin sun haɗa da mata bakwai da maza biyu.
CSP Muhammad Shehu, ya kuma ce, rundunar ƴan sandan ta samu nasarar ceto su ne ta hanyar samun bayanan sirri na wurin da ƴan bindigar suka ɓoye su.
