Labarai
Aliyu Magatakarda Wamakko ya lashe zaɓen Sanatan Sokoto ta Arewa
Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko, ya sake lashe zaɓen sanatan mazaɓar Sokoto ta Arewa, a zaɓen cike gurɓi da aka gudanar jiya Asabar.
BBC ta ruwaito cewa, Wamakko, ya samu nasarar ne a kan mataimakin gwamnan jihar Mannir Muhammad Ɗan’iya.
Aliyu Magatakarda Wamakko, ya samu ƙuri’a 141,468 yayin da abokin takararsa Mannir Ɗan’iya ya samu ƙuri’u 118,445.
