Labarai
NNPP ta yi watsi da sakamakon zaɓen cike gurbi na Kano
Jam’iyyar NNPP, ta yi watsi da rahoton sakamakon zaɓen cike gurbi na jihar Kano da aka gudanar jiya Asabar.
A cewar Jam’iyyar, ba ta amince da sakamakon zaɓen ba ne saboda ta na zargin an aikata maguɗi a wasu wuraren da aka yi zaɓen.
BBC ta ruwaito cewa, Shugaban jam’iyyar a Kano Umar Haruna Doguwa, ya ce “Akwai abubuwa da dama da suka faru waɗanda suka sanya ba mu gamsu da sakamakon ba.”
Haka kuma, Ya yi zargin cewa an tayar da hankula a wurare da dama a lokacin zaben da aka kammala.
Ya kuma ce za su yi nazari tare da neman hanyar da za a bi wa ƴaƴan jam’iyyar na NNPP haƙƙinsu.
A sakamakon da INEC ta bayyana, jam’iyyar APC ta lashe mazabar dan majalisar wakilai na Tudun Wada da Doguwa, yayin da NNPP kuma ta samu nasara a karamar hukumar Fagge.
Haka kuma ta ƙara da bayyana cewa, a zaɓen ƴan majalisun dokokin jiha goma sha hudu inda jam’iyyar APC ta samu goma da Gezawa da Tudun Wada da Gwarzo da Makoda da Dambatta da Warawa da Gaya da Dawakin Tofa da kuma Takai da Wudil.
NNPP ta samu kujeru hudu, wadanda suka hada da Ugogo da Gabasawa da Ajingi da kuma Garko.
