Labarai
Bauchi: Rikici Kan Nadin Sarauta Ya Yi Sanadin Rasa Rai Da Jikkatar Mutane Da Dama
Wani dattijo mai shekaru 70 a ranar Asabar din da ta gabata ya rasa ransa a wani rikicin kabilanci da ya barke a kauyen Sang da ke karamar hukumar Bogoro a jihar Bauchi, kan nadin sarautar wani kauye.
Mutane da dama, ciki har da wani tsoho mai shekaru 65, sun samu raunuka daban-daban a yayin da lamarin ya faru da misalin karfe 7 na dare.
Kazalika an kona gidaje 64 da babura uku da wasu kayyaki na miliyoyin naira.
Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi a wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar Ahmed Wakil ta fitar ranar Lahadi ta tabbatar da faruwar lamarin.
Sanarwar ta bayyana cewa “ CP ya bada umarnin gudanar da cikakken bincike, yana yin taka-tsan-tsan game da duk wani hali na durkushewa game da hargitsin zaman lafiyar jama’a a Bogoro.”
Wakil, Sufuritanda na ‘yan sanda, ya ce, bayan da rundunar ta samu labarin tashe tashen hankulan, an tura jami’anta da suka hada da Tactical teams, Rapid Response Squad da Operation Restore Peace zuwa yankin domin tabbatar da doka da oda.
Ya ce kwamishinan ‘yan sandan jihar, Aminu Alhassan, ya bayar da umarnin gudanar da bincike domin gano musabbabin rikicin.
Kakakin ‘yan sandan ya ce zaman lafiya ya dawo a yankin, ya kuma kara da cewa CP ya bukaci mazauna yankin da su kwantar da hankula.
Ya ce, “A ranar 15 ga watan Afrilun 2023, da misalin karfe 7 na yamma, rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta samu kiran wayar daga jama’a game da tashe-tashen hankula da ke faruwa a yankin Bogoro na jihar.
“Bincike na farko ya nuna cewa rikicin kabilanci a kauyen Sang na karamar hukumar Bogoro ya samo asali ne daga nadin sarautar Hakimin Sang.
“Wasu matasa da suka fusata da ayyuka daban-daban sun yi zanga-zangar adawa da nadin sarautar. A sakamakon haka, hakan ya haifar da kai hari kan ‘yan garin da ba su ji ba ba su gani ba, yayin da matasan da suka fusata suka kona gidaje 64, babura uku da kuma kayayaki na miliyoyin naira.
“Mutum daya mai suna Apollos Danlami mai shekaru 70 ya mutu a lamarin, yayin da wata Naemiya Bature mai shekaru 65 da kuma wasu mutane suka samu raunuka.”
Jaridar Punch ta rawaito cewa Wakil ya ce a halin yanzu ‘yan sanda suna sintiri a yankin da lamarin ya shafa domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali.
Ya kara da cewa ana ci gaba da kokarin ganin an gurfanar da wadanda suka aikata laifin.
