Labarai
Annobar Sankarau Ta Hallaka Mutane 18 A Wasu Jihohin Najeriya
Annobar cutar Sankarau ta kashe mutane 18 a cikin jihohi 22 na Najeriya, daga watan Oktoban Bara zuwa farkon Afrilun da muke ciki.
Wasu bayanai da hukumar kare yaɗuwar cututtuka ta kasa ta fitar jiya Asabar ya nuna kananan hukumomin 29 abin ya shafa kawo yanzu.
Jihohin 22 da aka bada rahoton bullar cutar Inji Hukumar sun haɗar da: Kano, Abia, Adamawa, da Bauchi, Bayelsa Benue, Borno, da kuma Ebonyi.
Sauran sune Jihar Gombe, Imo, Jigawa, Katsina, Kebbi, Kogi, Nassarawa, Niger, Oyo, Plateau, Sokoto da kuma Taraba sai Yobe da jihar Zamfara.
Masana sharhin lafiya dai sun ce yanayin zafi da ake fama da shi a yan kwanakin nan a wasu jihohin arewacin kasar nan shi ke kara ta’azzarar yaɗuwar cutar.
