Labarai
Shugaba Muhammadu Buhari zai tafi Ghana
Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai tafi kasar Ghana domin halarci taron ƙoli na shugabannin ƙasashen yankin tekun Guinea da za a gudanar a Accra babban birnin ƙasar Ghana.
Hakan na ƙunshe ne ta cikin wani saƙo da fadar shugaban ƙasar ta wallafa a shafinta na Tuwita, ta ce shugaban zai bar gida Najeriya a yau Talata, wanda shugaban ƙasar Ghana Nana Akuffo-Ado zai jagoranci taron.
Haka kuma, sanarwa ta ruwaito cewa, yayin taron, shugaba Buhari zai gabatar da jawabin da zai tattauna dabarun ƙarfafa zaman lafiya da tsaro da yaƙi da masu aikata miyagun laifuka a gaɓar tekun yankunan ƙasashen.
Ta cikin sanarwar dai, an bayyana cewa shugaba Muhammadu Buhari, zai samu rakiyar ministan harkokin ƙasashen ƙetare Geoffrey Onyeama da mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Babagana Monguno mai ritaya, da daraktan hukumar tattara bayanan sirri ta Amb. Ahmed Rufai Abubakar da sauran jami’an gwamnati.
