Connect with us

Labarai

FG Ta Yi Bayani Kan Kwaso Yan Najeriya Daga Masar Da Suka Makale A Sudan

Gwamnatin tarayya ta ce an share jirgin saman Najeriya NAF C-130H da jirgin Air Pace a Masar domin kwaso ‘yan Najeriya da suka makale a Sudan.

Gwamnatin ta tabbatar da hakan ne a wata sanarwar hadin gwiwa da Sakatarorin Ma’aikatar Harkokin Waje, Ambasada Janet Olisa, da na harkokin jin kai, Dr Sani Gwarzo a Abuja.

“An kammala shirye-shiryen jigilar duk ‘yan Najeriya da suka tsere da kansu zuwa wasu kasashen da ke makwabtaka da Sudan.

“Duk da haka, an tanadi motocin bas guda arba’in a Sudan domin jigilar daliban da sauran ‘yan Najeriya daga Khartoum zuwa iyakar Aswan na kasar Masar, wanda daya ne daga cikin iyakokin da aka gano lafiyayyan hanya, domin a lokacin wannan bayanin, bas din farko sun tashi daga Khartoum. ”in ji sanarwar.

Sai dai gwamnatin tarayya ta ce an warware matsalar tun farko a lokacin jigilar daliban Najeriya da suka makale daga birnin Khartoum inda direbobin motocin bas suka tsaya suka sauke daliban saboda rashin biyan kudin sufuri.

“An ba wa wasu daliban Najeriya da suka samu hanyar zuwa kan iyakar Habasha izinin shiga kasar Habasha, biyo bayan shiga tsakanin da wasu shugabannin Najeriya suka yi.

“Daliban suna cikin koshin lafiya. Hakazalika, wani rukunin ‘yan Najeriya da gwamnatin Hadaddiyar Daular Larabawa ta taimaka sun isa Jeddah a Saudiyya kuma an shirya mayar da su gida,” inji ta.

Gwamnati ta ce tuni ta tuntubi wani daki mai zaman kansa don sanya ido kan aikin kwashe mutanen.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa Ya bayyana cewa dakin halin da ake ciki yana karkashin jagorancin babban sakatare na ma’aikatar jin kai ta tarayya. (NAN)

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet