Connect with us

Labarai

Jami’an Tsaro Sun Kama Masu Garkuwa Tare Da Ceto Wani Mutanen Da Aka Sace

 

Jami’an tsaro na hadin gwiwa sun damke wasu ‘yan kungiyar masu garkuwa da mutane uku a karamar hukumar Aguata ta jihar Anambra.

An kama wadanda ake zargin ne da yammacin ranar Alhamis, bayan wani artabu da jami’an tsaro a yankin.

An bayyana sunayensu da Chinonso Offor, dan jihar Enugu, mazaunin Ekwulọbịa, Hycent Ugwuike, dan asalin Nsukka, mazaunin Onitsha da Samuel Sunday daga Akwa-Ibom amma mazaunin Isuochi, jihar Abia.

A cewar jami’an tsaron, “Bayan musayar wuta da bindiga, jami’an tsaron sun kuma ceto wadanda aka yi garkuwa da su a Neni ta hanyar Okacha Junction.

“Aka-47 guda biyu dauke da harsashi mai rai, kayan ‘yan sanda da na sojoji na jabu, wayoyin hannu guda biyu, riguna masu tare harsashi guda biyu, motocin tafiya guda biyu, bakar Prado Jeep guda daya mai lamba: GWA – 696 CM ABUJA, Ash Lexus 350 daya mai lamba: An kwato EKY – 605GV LAGOS da sauran su.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai a ranar Asabar din nan, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Tochukwu Ikenga, ya ce ‘yan ta’addan sun shaidawa jami’an ‘yan sandan jihar Anambra cewa su ‘yan asalin yankin Biafra ne.

Jaridar Punch ta rawaito cewa Ikenga ya kara da cewa “har yanzu ‘yan bindigar na hannun ‘yan sanda, ana ci gaba da gudanar da bincike”.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahisgrandpashabetcasibom xcasibom xgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasibomholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet