Labarai
Albarkacin bikin ranar Ma’aikata: Ganduje ya yafe wa Malaman makaranta Bashi
Gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya yafe wa Malaman makaranta da suka shiga tsarin mallakar gidaje ta hanyar biya a hankali daga albashinsu, ragowar kuɗin da ba su gama biyan gwamnati ba.
Gwamna Ganduje, ya bayyana hakan ne yau Litinin ta cikin jawabinsa na bikin ranar ma’aikata a taron da aka gudanar a filin wasa na Sani Abacha da ke Ƙofar Mata.
Gwamnan, ya kuma yaba wa ɗaukacin ma’aikatan Kano bisa goyon baya da haɗin kai da suka ba shi wajen gudanar da mulki har tsawon shekaru 8.
Da yake gabatar da jawabi a taron, shugaban kungiyar Kwadago reshen Kano kwamared Kabiru Inuwa, ya buƙaci gwamnatin jihar Kano da ta hanzarta magance matsalolin da ƴan ƙwadago da kuma ƴan fansho ke fuskanta.
