Labarai
An Kwashe Ragowar ‘Yan Najeriya 1,300 Da Suka Makale A Sudan — NANS
Kungiyar daliban Najeriya ta kasa da ke karatu a Sudan ta bayyana cewa ‘yan Najeriya 1,300 da suka makale sun bar birnin Khartoum a ranar Lahadi.
Hakan na kunshe ne a wata takarda mai dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na NANS, Amal Pantami, ya fitar a ranar Lahadi.
Jaridar Punch ta rawaito cewa Sai dai wasikar ba ta bayyana inda ‘yan Najeriya da suka makale za su dosa ba; ko dai Aswan ko kuma Port Sudan.
Wasikar ta ce, “Wannan don sanar da jama’a ne cewa an kwashe sauran daliban Najeriya daga Khartoum a yau Lahadi 30 ga watan Afrilun 2023.
“Motar bas bas guda 26 ne kuma kowace motar bas ta ƙunshi mutane kusan 50.
“Muna ci gaba da neman addu’ar kowa da kowa kuma muna fatan dukkan daliban za su isa Najeriya lafiya.
“Muna godiya ga ci gaba da goyon baya da addu’o’in ku.”
