Labarai
Da ɗumi-dumi: Ƴan sanda sun cafke dakataccen Kwamishinan zaɓe na Adamawa
Rundunar ƴan sanda ta ce, ta cafke dakataccen kwamishinan zaɓen jihar Adamawa Hudu Ari.
Rundunar ta bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa da mai magana da yawunta CSP Olumuyiwa Adejobi, ya fitar da yammacin yau Talata.
Sanarwar ta ce, jami’an ƴan sanda masu bibiyar harkokin zaɓe ne suka kama Hudu Ari, yau a birnin tarayya Abuja.
Sanarwar ta ƙara da cewa, dakataccen kwamishinan na INEC na hannun ƴan sanda domin amsa tambayayoyi kan tuhume-tuhumen da ake masa game da ayyana Sanata Aishatu Binani a matsayin wadda ta lashe zaɓen cike gurbi da aka gudanar ranar 15 ga watan Afrilu.
