Labarai
Bana Nadama Akan Ayyana Binani Ce Ta Ci Zabe – Dakataccen REC Na Adamawa
Dakataccen Kwamishinan zabe a Hukumar zabe mai zaman kanta ta Kasa (INEC) a jihar Adamawa Barista Hudu Yunusa Ari, ya ce bai yi nadamar bayyana Sanata Aishatu Dahiru Binani a matsayin wadda ta lashe zaben gwamna a jihar ba.
Sai dai ya musanta zargin da ake yi masa na karbar cin hancin Naira biliyan 2 domin bayyana hakan.
Binani ta kasance yar takarar gwamna na jam’iyyar APC a jihar Adamawa a zaben 2023.
Ta kalubalanci gwamna mai ci kuma dan takarar jam’iyyar PDP Ahmadu Umaru Fintiri wanda a karshe hukumar ta ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben bayan kammala zaben.
A wata hira da ya yi da BBC Hausa a ranar Talata, Hudu ya ce bai yi nadamar bayyana sakamakon zaben ba duk da ba a kammala tattara sakamakon ba.
Hudu ya ce doka ta ba shi ikon bayyana sakamakon zaben, inda ya ce a shirye yake ya mika kansa ga rundunar ‘yan sandan Najeriya da ta gayyace shi.
“Ban nemi kobo daya a matsayin cin hanci daga Fintiri ko Binani ba. Na san karbar cin hanci haramun ne. Na rantse zargi ne kawai. Me zan yi da Naira biliyan2? Na kuma ga hakan a shafukan sada zumunta,” in ji shi.
Da aka tambaye shi ko ya yi nadamar abin da ya aikata, Hudu ya ce, “Na ce maka ban yi dlnadama ko kadan, idan ka yi wani abu kamar yadda doka ta tanada, babu nadama. A kan gayyatar ‘yan sanda, dole ne in girmama shi, kada in boye, “in ji shi.
