Labarai
Wasu Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 2, Sun Yi Garkuwa Da Hudu A Kaduna
Mutane biyu ne ake fargabar sun mutu a daren ranar Litinin bayan da wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne suka kai hari a unguwar Kofar Kona da ke cikin birnin Zariya a jihar Kaduna.
Majiyoyi sun ce ‘yan bindigar sun isa yankin ne a kafa da karfe 9:40 na dare inda suka wuce gidan wani jami’in kwastam.
Wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunansa ya ce ‘yan bindigar da suka zo da yawa sun kai farmaki gidan wani jami’in kwastam mai suna Malam Abubakar Modibbo inda suka yi garkuwa da matarsa Asiya Abubakar tare da ‘ya’yansa mata guda biyu, Khadijatul Kubra da Hafsat tare da Falalu Ibrahim.
“’Yan bindigar sun kuma harbe wani Zaharaddeen Mohammed na Amaru da Sunusi Sani na Dorayi wanda ya zo wucewa.
“Daga baya an ruwaito Sani ya mutu da safe a asibiti sakamakon raunukan da ya samu daga harbin bindiga.”
Wani dan kungiyar ‘yan banga ya ce ‘yan bindigar da suka nufi kauyen Dorayi da ke wajen Zariya, sun yi awon gaba da wasu shanu. A cewarsa, sun kuma yi awon gaba da mutane da dama wadanda adadinsu ya kai 20.
Ya ce ‘yan bindigar sun yi watsi da duk wadanda suka yi garkuwa da su a yankin, suka koma daji, bayan sun yi artabu da jami’an tsaro.
Dan bangan ya bayyana cewa ‘yan bindigar sun kona gidan wani Alhaji Dalha da babura guda biyu kafin su tsere saboda musayar wuta da suka yi.
Kokarin jin ta bakin jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna, DSP Mohammed Jalige ya ci tura saboda wayarsa bata shiga.
