Connect with us

Ilimi

Musabaka: Wata Daliba Ta Rabauta Da Kyautar Gida Da Makudan Kudi A Kano

 

Gwamnatin jihar Kano ta yi alkawarin bayar da sabon gida da tsabar kudi Naira miliyan 3 ga wata ‘yar asalin jihar, Aisha Abubakar Dorayi, wadda ta zama ta biyu a gasar Karatun Al-Qur’ani ta duniya ta shekarar 2022, wadda aka gudanar a kasar Hadaddiyar Daular Larabawa, Dubai.

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya yi wannan alkawarin ne a yayin taron majalisar zartarwa ta jiha a gidan gwamnati dake Kano.

Ya ce shawarar da aka yanke na baiwa wanda ta yi nasara kyautar shi ne don karfafa wa sauran ‘yan asalin jihar kwarin gwiwa don ganin sun yi fice.

“Wannan nasara ba ga Aisha kadai ba, ba ga iyayenta kadai ba, a’a ga jihar Kano ne. Don haka ne muka yanke shawarar zaburar da ita da kyautar gida a cikin gidajen malamai na jihar. Mun kuma yanke shawarar bayar da tsabar kudi Naira miliyan uku ga yarinyar. Muna alfahari da ita,” in ji Ganduje.

Da take jawabi bayan sanarwar, wacce ta lashe kyautar, Aisha Abubakar Dorayi daga karamar hukumar Gwale ta jihar ta yaba da wannan karimcin tare da yin alkawarin dorewar wannan aiki.

Ta godewa iyayenta da malamanta da abokan aikinta da suka karfafa mata gwiwa don samun ilimi har zuwa irin wannan matakin.

“Na yi matukar farin ciki a yau da gwamnatin jihar ta amince min da wannan nasarar. Amma nasara tamu ce, musamman malamaina da iyayena. Sun tsaya tare da ni don cimma wannan a yau. Ba zan iya gode musu ba. Allah ya saka musu da alkahair duka,” ta yi godiya.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahisgrandpashabetcasibom xcasibom xgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasibomholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet