Connect with us

Labarai

Yan Sanda Sun Tabbatar Da Bada Belin Dakataccen Kwamishinan Zaben Adamawa

 

Rahotanni daga rundunar Yan sanda sun nuna cewa an bayar da belin Kwamishinan Zabe na jihar Adamawa Hudu Yunusa-Ari, wanda ‘yan sanda ke bincikensa.

Biyu daga cikin kwamishinonin da jami’an hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) da ake yi wa tambayoyi a hedikwatar ‘yan sanda dangane da batun zaben gwamnan Adamawa sun samu damar zuwa.

An bayar da belin su ne bisa wasu sharudda, kuma za a ci gaba da gudanar da bincike kan laifin da suka aikata.

Daga cikin sharudan dole ne su ajiye fasfo din tafiye tafiyen su; kuma an takaita zirga-zirgar su a cikin babban birnin tarayya (FCT).

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa wani Sanata ne ya tsaya Yunusa-Ari bayan an yi masa tambayoyi na tsawon kwanaki uku a hannun ‘yan sanda.

Sufeto Janar na ’yan sanda Alkali Baba ya kuma yi wa REC, kwamishinonin na kasa tambayoyi da kan sa.

Yunusa-Ari, a cewar majiyoyi sun yi musayar kalamai da kwamishinonin INEC kan ikirarin cewa ya gudu ne domin neman mafaka.

Zaman ya gudana ne kan zarge-zargen cin hanci da rashawa a zaben da aka yi a ranar 15 ga watan Afrilu, bayan da REC ya ayyana yar takarar jam’iyyar APC Ayisetu Dahiru Binani a matsayin zababbiyar gwamna, ana tsaka da tattara sakamakon zaben.

Da Vanguard ta tuntubi jami’in hulda da jama’a na rundunar (FPRO), Muyiwa Adejobi, ya ce laifi ne da za a iya bayar da belinsa kuma ya yi alkawarin yin cikakken bayani ga jaridar daga bisani.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet