Labarai
INEC Har Yanzu Ba Ta Karbi Kudiri Daga Majalisa Kan Goge Bayanan Masu Zabe Ba – Kakakin Hukumar
Hukumar zabe mai zaman kanta ta Kasa INEC ta ce har yanzu ba ta samu wani kuduri na majalisar wakilai da ke cewa hukumar ta cire sunayen ‘yan Najeriya da suka mutu da wadanda suka ki kada kuri’a a zabukan da aka gudanar na kasa.
Jarudar Punch ta ruwaito cewa, majalisar ta yi kira ga alkalan zaben da su cire sunayen matattun ‘yan Najeriya daga cikin rajistar masu kada kuri’a.
Majalisar ta yi wannan kiran ne a zamanta na ranar Alhamis biyo bayan amincewa da wani kudiri na gaggawa da wani dan majalisa Leke Abejide ya gabatar.
Da yake mayar da martani, mai magana da yawun shugaban hukumar ta INEC, Rotimi Oyekanmi, ya ce a ranar Juma’a, “An ja hankalinmu kan rahotannin kafafen yada labarai na kudurin da majalisar wakilai ta zartar a jiya, na neman INEC ta dauki wasu matakai kan rajistar masu zabe ta kasa.
“Duk da haka, ya kuma zama al’adar majalisa ta mika irin wadannan kudurori a hukumance tare da cikakkun bayanai kan abubuwan da suka wakana ga hukumar a duk lokacin da aka zartar da wasu kudurori don baiwa INEC damar daukar matakan da ake bukata.
“Amma har yanzu hukumar ba ta samu wata sanarwa daga majalisar ba game da hakan. Don haka ba zan iya mayar da martani ba bisa rahotannin da kafafen yada labarai ke yadawa.”
