Connect with us

Labarai

Ƴan Sanda Sun Cafke Magidancin Da Ya Kashe Tsohuwar Matarsa

Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa, a ranar Asabar, ta samu nasarar damke wani magidanci mai suna Aminu Abubakar, mai shekaru 56, bisa zarginsa da lakadawa matarsa ​​mai shekaru 38 da haihuwa dukan tsiya.

Wanda ake zargin, mazaunin Lelewaji, Shagari Phase 2, a karamar hukumar Yola ta Kudu, ya kashe Nana Fadimatu, kwana guda kafin aurenta da sabon saurayin nata.

A binciken da ‘yan sanda suka yi, ya nuna cewa wanda ake zargin ya dade suna tafka rikicin aure da marigayar.

An kuma samu labarin cewa su biyun sun amince su rabu da juna.

Sai dai kuma an ce Abubakar bisa ga tsananin kishin sa daya motsa kwatsam bayan ya samu labarin cewa matarsa ​​da take kwana a gidansa zata auri wani Mahmud Rufa’i.

Bisa hakanne batare da bata wani lokaci ba yasa tabarya ya shekata.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Suleiman Nguroje, ya ce, “Abin da ya fusata da labarin cewa Nana za ta auri sabon miji ne, wanda ake zargin ya gayyaci tsohuwar matar tasa da misalin karfe 10 na dare wanda za’a daura mata aure a ranar 5 ga watan Mayu, 2023, inda ya shekata mata mari tare da dukanta da tabaraya sakamakon haka ta fadi a sume kuma daga baya aka ce ta mutu.”

Nguroje ya ce wanda ake zargin da aka kama, za a gurfanar da shi gaban kuliya bayan an tuhume shi.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahisjojobetholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet