Labarai
CISLAC ta koka kan bashin Dala miliyan 800 da gwamnatin Tarayya ta karɓo
Ƙungiyar nan ta CISLAC mai rajin sanya ido kan ayyukan majalisar dokoki, ta koka kan bashin dala miliyan ɗari takwas da gwamnatin Tarayya ta karɓo daga bankin duniya domin rage raɗaɗin cire tallafin man fetur.
Ƙungiyar dai, ta bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa da ta fitar, a yau Litinin.
A cewar ƙungiyar yin hakan baƙon al’amari ne saboda idan an daina bayar da tallafin tun a watan Afrilu, to ya kamata a mayar da kuɗaden da gwamnatin ta karɓo daga bankin na duniya.
A cewar shugaban ƙungiyar Awwal Musa Rafsanjani, a ganinsu, idan aka karɓo bashi kamar yadda doka ta tanada, ya kamata a ce an yi amfani da shi wajen samar da ayyukan da za su amfani ƙasa.
Haka kuma ya ƙara da cewa, “Bashin da aka karɓo lokacin da gwamnati za ta miƙa mulki abin damuwa ne saboda ba a san ma ko gwamnatin da za ta zo, ko za ta amince ta ci gaba da waɗannan tsare-tsare ba.”
