Labarai
Duba lafiyar haƙora ya sanya shugaba Buhari ɗaga ranar dawowa Najeriya
Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya tsawaita zamansa a birnin London da sati ɗaya domin a duba lafiyar haƙoransa.
Mai magana da yawun shugaba Buhari Femi Adesina, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar.
Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya je London ne domin halartar bikin naɗin sarkin Ingila, charles lll.
Da farko dai, an tsara cewa shugaban zai dawo gida Najeriya ne a cikin makon nan, sai dai yanzu zai ƙara mako guda domin ganawa da likitan haƙoransa, wanda tuni ya fara duba shi.
”Likitan nasa ya buƙaci ya ƙara ganinsa nan da kwana biyar domin ci gaba da lura da yanayin haƙoran nasa”, a cewar Femi Adesina.
