Uncategorized
Tinubu zai yi balaguro zuwa nahiyar Turai
Yayin da ya rage ƙasa da kwanaki 20 ya sha rantsuwar kama aiki a matsayin shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu zai yi bulaguron aiki zuwa Turai yau Laraba.
Ofishin sabon zaɓaɓɓen shugaban ne ya bayyana rahoton balaguron nasa ta cikin wata sanarwa da ya fitar yau Laraba..
Sanarwar ta ce, Bola Ahmed Tinubu, zai yi amfani da bulaguron domin lura da shirye-shiryen miƙa mulki da tsare-tsarensa, ba tare da fuskantar wata damuwa ko kuma yawan ɗauke hankali ba.
Haka kuma sanarwar ta ce, ”Yayin ziyarar, sabon shugaban mai jiran gado zai gana da masu zuba jari da manyan abokan hulɗar kasuwanci domin samar da damar zuba jari a Najeriya ƙarƙashin mulkinsa.”
