Labarai
Hukumar EFCC ta cafke tsohon Ministan lantarki
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC, ta kama tsohon Ministan hasken lantarki Engr. Saleh Mamman.
Jami’an hukumar sun cafke shi ne bisa zarginsa da yin sama da faɗi da kuɗi kimanin naira biliyan Ashirin da biyu da aka ware, domin inganta samar da hasken lantarki.
Daily Trust ta ruwaito jami’an EFCC ɗin, sun cafke tsohon Ministan ne a Larabar makon nan domin ya amsa tambayoyi a kan yadda kuɗaɗen suka salwanta.
Kuɗin dai an ware su ne don gudanar da aikin samar da wutar lantarki a Zungeru da Mambilla, sai dai, ana zargin Ministan da wasu manyan jami’an ma’aikatar lantarki da wawushe kuɗin.
