Wasu ƴan bindiga, sun sace manoma da dama a ƙauyen Kaffin-Koro da ke yankin ƙaramar hukumar Paikoro ta jihar Neja.
A zantawar wasu mazaunan ƙauyen da manema labarai, sun ce ƴan bindigar sun yi fiye da sa’o’i biyu suna harbe-harbe, inda hakan ta sanya mazauna ƙauyen tserewa domin neman mafaka.
Haka kuma sun bayyana cewa, ɓata garin sun kai hari ne ranar Larabar makon nan da har harin ya yi sanadiyyar rasuwar mutum guda.
Sai dai BBC ta ce, babu cikakkun bayanai kan adadin manoman da aka yi garkuwa da su, sai dai yankin Neja na daga cikin yankunan Najeriya da ke fama da hare-haren ‘yan bindiga domin neman kudin fansa.
