Labarai
Gwamnatin tarayya ta fara tattara alƙaluman marasa aikin yi
Hukumar samar da aikin yi ta Najeriya NDE, ta fara tattara alƙaluman mutanen da ba su da aikin yi.
Shugabar hukumar shiyyar jihar Enugu Ifeoma Ezekwe, ce ta bayyana hakan a ganawarta da manema labarai ranar Juma’ar da muka yi ban kwana da ita.
Ta ce ana gudanar da rajistar ne domin sanin ƙididdigar ‘yan Nigeria da ba su da aikin yi , wanda ta hakan ne za a san yadda za a tallafa musu.
Ta ƙara da cewa, an fara aikin rajistar marasa aikin yin a dukkanin jihohi 36 da kuma birnin tarayya Abuja.
Shugabar, ta ce, ana yin aikin ne a lokaci guda a dukkanin ƙananan hukumomi 774 dake faɗin Nigeria.
