Labarai
Masu safarar ƙwayoyi 2 sun kasayar da ƙulli 193 na Cocaine a komar NDLEA
Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta NDLEA, ta ce, ta cafke mutane 185 a birnin tarayya Abuja da kuma jihar Kano, bisa zarginsu da safarar miyagun kwayoyi.
Mai magana da yauwn hukumar Mr. Femi Babafemi, ne byyana hakan ne ta cikin wata sanarwa da ya fitar da yammacin jiya Lahadi.
Sanarwar ta ce, wasu ‘yan kasuwa biyu da ke tsare a hannunta, kwana uku bayan kama su a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke birnin tarayya Abuja, sun kasayar da kulli 193 na hodar Ibilis.
Haka kuma ya kara da cewa, wadanda aka cafke din masu suna Onoh Ebere, mai shekaru 49 da Christian Ifeanyi, mai shekaru 47 sun fada komar hukumar ne a ranar 10 ga wannan watan na Mayu.
Jami’in, ya kuma ce jami’an hukumar sun kama su ne yayin da suka dawo daga kasar Uganda bayan baro birnin Addis Ababa, ta cikin jigin Ethiopian Airlines mai lamba ET 951.
