Labarai
Kwankwaso da Tinubu sun gana a Paris
Sabon zaɓaɓɓen shugaban Najeriya Bola Ahamad Tinubu, ya gana da ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen da ya gabata na jam’iyyar NNPP Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.
Jaridar Solacebase ta rawaito cewa, jagororin sun shafe tsawon sa’o’i suna ganawa ranar Litinin a Paris babban birnin ƙasar Faransa.
Haka kuma ta bayyana cewa, mai ɗakinsa Kwankwaso tare da ɗan majalisar tarayya na jam’iyya Abdulmimin Jibrin Kofa, na daga cikin waɗanda suka raka Kwankwso wajen taron, ya yin da kuma aka shiga taron da matar Tinubu da kuma shugaban majalisar wakilan Najeriya, Femi Gbajabiamila.
Rahotonni sun ce, An fara ganawar da misalin ƙarfe 12:30 har zuwa 4:45, inda ganawar tasu ta samu halartar shugaban majalisar wakilan Najeriya.
