Labarai
Yadda MTN ya sauya lambobin amfanin yau da kullum
Kamfanin sadarwa na MTN, ya sauya sababbin lambobin amfanin yau da kullum da ake amfani da su.
Yanzu haka dai bayan fara aiki da lambobin, kamfanin na MTN, ya dakatar da duka tsoffin.
Ga yadda sababbin Code ɗin suke:
Idan zaka loda kati a Layin ka sai ka danna *311*Pin# maimakon *555*Pin#.
Idan zaka duba kuɗin da ke cikin layinka watau Checking balance: *310# maimakon *556#
Idan Zaka aro Kuddi:
*303# maimakon *606#
Idan zaka sayen data:
*312# Maimakon *131#
