Labarai
Kutu tasoke sahalewar takarar zababban Govna
Wata babban Kotun tarayya da ke zamanta a jihar Kano bisa jagorancin Mai Shari’a Muhammad N Yunusa ta soke zaben sahalewar takarar zababben gwamnan Jihar Abia, Dakta Alex Otti, da dukkanin ‘yan takarar jam’iyyar Labour Party a jihohin Abia da Kano.
Kotun ta yanke hukuncin cewa nasarar da suka samu na fitowa a dama da su a babban zaben 2023 ya gudana ne ba tare da bin dokoki da ka’idojin dokar zabe ta 2022 ba.
Kotun ta ce, gazawa da rashin turawa da mika jerin sunayen mambobin jam’iyyar LABOUR PARTY da ita jam’iyyar ta kasa yi zuwa ga hukumar INEC cikin kwanaki 30 kafin gudanar da zaben fitar da gwani na jam’iyyar ya nuna cewa hanyoyin da jam’iyyar ta bi basu inganta ba.
