Labarai
Shugaba Buhari ya amince da naɗin mace ta farko a muƙamin Akanta Janar
Shugaba ƙasa Muhammadu Buhari, ya amince da naɗa Uwar gida Oluwatoyin Sakirat Madein a matsayin sabuwar Akanta Janar ta Najeriya.
Amincewa da naɗin nata na ƙunshe ne ta cikin wata sanarwa da shugabar ma’aikata ta tarayya Dakta Folasade Yemi-Esin ta fitar yau Juma’a a birnin tarayya Abuja.

Sanarwar ta ce, shugaba Buhari, ya amince da naɗin nata ne nan take.
Rahotonni sun bayyana cewa, Oluwatoyin Sakirat ƴar asalin ƙaramar hukumar Ikenne ta jihar Ogun ce.
Haka kuma, an kuma haife ta a ranar 7 ga watan Maris ɗin 1965.
Uwar gida Oluwatoyin Sakirat Madein yanzu haka ta zama mace ta farko da ta riƙe wannan muƙami a tarihin Najeriya.
