Kasuwanci
Shugaba Buhari ya ƙaddamar da Sabuwar Matatar Mai ta Dangote
Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya ƙaddamar da Sabuwar matatar mai ta Aliko Dangote yau Litinin a jihar Lagos.
Shugaban, wanda ya samu rakiyar shugabannin ƙasashen Afrika 5 ya ƙaddamar da matatar wadda za ta riƙa tace ganga 650,000 a kowacce rana.
Sabuwar Matatar ta Aliko Dangote dai ita ce mafi girma a nahiyar Afirka.
Matatar, wadda aka gina ta a yankin Lekki da ke birnin na Lagos, ana sa ran za ta kawo ƙarshen matsalar mai a Najeriya.
