Labarai
Sokoto: Mutane 4 sun rasu sakamakon fashewar Tukunyar Gas
Rundunar ‘yan sandan jihar Sokoto, ta tabbatar da rasuwar mutane hudu sakamakon fashewar wata tukunyar gas a shagon mai sana’ar walda da ke karamar hukumar Isa ta jihar.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar DSP Sunusi Abubakar ne ya tabbatar da hakan ga manema labarai bayan faruwar lamarin da yammacin ranar Lahadi.
Haka kuma ya kara da cewa, fashewar Tukunyar Gas din ba ta da nasaba da matsalar tsaro da jihar ke fuskanta.
DSP Sunusi Abubakar, ya kuma ce, an samu jikkatar mutane uku sakamakon iftila’in baya ga wadanda suka rasu.
Shi ma a nasa bangaren, shugaban karamar hukumar ta Isa Abubakar Danali, ya tabbatar da faruwar iftila’in sai dai ya ce, bai san adadin asarar da aka samu ba sakamakon fashewar kasancewar lamarin ya faru ne a lokacin ba ya gari.
