Gwamna Abdulrazaq ya maye gurbin gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal, wanda wa’adin shugabancinsa zai cika a ranar 29 ga watan wannan watan da muke ciki na Mayu.
Hakan na ƙunshe ne ta cikin wata sanarwar da shugaban ƙungiyar mai barin gado Aminu Waziri Tambuwal ya sanya wa hannu a ƙarshen taron gaggawa na gwamnonin jihohi karo na 7 da suka gudanar a daren Talatar makon nan a birnin tarayya Abuja.
Sanarwar ta ce, an ayyana Abdulrazaq ne ta hanyar fahimtar juna yayin da aka zabi gwamnan jihar Oyo Seyi Makinde, a matsayin mataimakin shugaban kungiyar.
Haka kuma Sanatrwar ta ce “Mambobin ƙungiyar sun bayyana gamsuwarsu da nasarar da aka samu na naɗin sababbin gwamnoni da masu dawowa daga ranar 14 zuwa 19 ga Mayun bana”.
“Mambobin sun himmatu wajen ci gaba da yin hadin gwiwa a tsakanin jihohi ta hanyar inganta takwarorinsu, koyo a matakin kananan hukumomi da zurfafa dangantaka da gwamnatin tarayya da sauran cibiyoyi.
Jaridar Solacebase ta rawaito cewa, shugaban ƙungiyar, a yayin taron ya kuma sanar da mambobin ƙungiyar cewa Ministar kuɗi ta amince da bukatar kungiyar ta dakatar da ci gaba da cire kuɗi daga asusun jihohi domin biyan buƙatun ƙananan hukumomi wadanda suke na Paris Club, kuma kudaden da aka cire zuwa yanzu za a mayar da su ga jihohi.