Labarai
Jirgin Nigeria Air zai iso ranar Juma’a- Minista
Ministan sufuri na Najeriya, Sanata Hadi Sirika, ya bayyana cewa jirgin sama na kamfanin Nigeria AIR, zai iso ranar Juma’a mai zuwa.
Hakan na a matsayin wani lamari da zai zama babban ci gaba ga shirye-shiryen soma tafiyar da harkokin kamfanin.
A hirar da ya yi da gidan Talabijin na Channels, ministan ya ce, ana sa ran cewa jirgin zai iso ne cikin kwana biyu.
Ya yi alƙawarin cewa za a ƙaddamar da jirgin mai kalolin tutar Najeriya domin cika duka alƙawuran da gwamnatinsu ta yi a ɓangaren sufuri.
