Kano: Ƴan sanda sun cafke masu sace allunan Kabari
Rundunar ƴan sandan jihar Kano, ta cafke wasu da ake zargi da satar allunan makabarta 28 da ake yi wa kabari shaidar mamata.
Rundunar ta bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwar da ta fitar mai ɗauke nasarorin da ta cimma cikin kwanaki 12 da suka wuce, rundunar tace ta kama matasan dumu dumu suna karye allunan
A tattaunawar su da ɗaya daga cikin ɓarayin yace “Ina shiga Maƙabarta na yi satar Allunan Kabari da ƙarfe 03:00 na dare” inji matashin.
Bayan matsa masa da tambayoyi, matashin ya ce, idan ya sayar yana amfani da kuɗin ne wajen sayen abincin da zaici da kuma taba Sigari.