Labarai
Shugaba Buhari ya bai wa Tinubu da Shettima lambobin girma da muhimman takardun aiki
Shugaban ƙasa mai barin gado Muhammmadu Buhari, ya bai wa magajinsa Bola Ahmed Tinubu, lambar girma mafi daraja ta Najeriya watau Grand Commander of the Order of the Federal Republic GCFR.

Tashar Talabijin ta Channels, ta ruwaito cewa, shugaban ya basu lambobin girmamawar a birnin tarayya Abuja.
Wannan dai na a matsayin wani ɓangare na shirye-shiryen da ake yi na rantsar da sabuwar gwamnati a ranar Litinin 29 ga wannan watan da muke ciki na Mayu.

Haka kuma, yayin taron, shugaba Muhammadu Buhari, ya bai wa mataimakin shugaban ƙasa mai jiran gado Kashim Shettima lambar girma ta biyu watau Grand Commander of the Order of Niger GCON.
